An kashe 'yar jarida a Afghanistan

Image caption Anja ta mutu (Dama) Kathy na jinya (Hagu)

Wani dan sanda a Afghanistan ya harbe wata 'yar Jarida BaJamushiya, har lahira yayinda ake shirin gudanar da zaben shugaban kasa a ranar Asabar.

An harbe Anja Niedringhaus ne a cikin wani gini da aka killace saboda dalilan tsaro.

Abokiyar aikinta, Kathy Gannon, wadda 'yar Canada ce, ta samu raunika.

'Yan jaridar na cikin wani ayarin motoci ne dake rarraba takardun zabe a lardin Khost, kusa da iyaka da Pakistan.

Sai dai kakakin ma'aikatar cikin gida ta Afghanistan din, Sidiq Siddiqi, ya ce ga alama dan sandan ya yi harbin ne bisa kuskure.

Sojoji dubu dari 4 ne da suka hada da na kasashen waje, aka girke a duk fadin kasar ta Afghanistan domin samar da tsaro a lokacin zaben shugaban kasar da za a yi a ranar Asabar.

'Yan kungiyar Taliban dai sun yi barazanar kawo cikas ga zaben.

Karin bayani