'A binciki kashe Sheikh Makaburi na Kenya'

Image caption Margayi Sheikh Abubakar Shariff Ahmed

Kungiyar kare Hakkin Bil-Adama ta Human Rights Watch ta yi kira ga hukumomin Kenya da su gudanar da bincike kan kisan wani malamin addinin Musulunci mai tsattsauran ra'ayi.

A ranar Talata ne dai wasu 'yan bindiga da ba a san ko su wanene ba, suka harbe Sheikh Abubakar Shariff Ahmed, wanda ake yiwa lakabi da Makaburi, a birnin Mombasa.

Bayan sallar Juma'a, an yi artabu na gajeren lokaci tsakanin 'yan sanda da wasu matasa dake zanga-zangar nuna adawa da kisan malamin.

'Yan sanda dai sun zargi Sheikh Abubakar Shariff Ahmed da daukan matasa domin su shiga kungiyar al Shabaab.

A wata hira da BBC a baya, malamin ya ce an yi barazanar kashe shi, amma hakan ba zai sa ya yi kasa a gwiwa ba.

Karin bayani