Ramsey zai buga wasa da Everton

Aaron Ramsey da Arsene Wenger Hakkin mallakar hoto Premier League
Image caption Aaron ya yi jinyar watnni uku

Manajan kulob din Arsenel, Arsene Wenger ya ce dan wasan tsakiya Aaron Ramsey ya komo fagen daga, inda zai shiga tawagar kungiyar da za ta kara da Everton.

A ranar Lahadi mai zuwa ne dai za a yi karawar ta gasar premier League, a filin wasan Goodison park.

Dan wasan kasa da kasa na yankin Wales mai shekaru 23 ya zura kwallaye 13 a wasanni 27, kafin ya samu rauni a cinya, a wasan da suka kara da West Ham 3-1 a watan Disambar da ta wuce.

"Samun dan wasa kamar Ramsey da zai taimaka wa tawagar ta samu nasara, abu ne mai muhimmanci." In ji Wenger.