Mahara sun kashe mutane 22 a Zamfara

Wasu sojojin Najeriya Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Rahotanni sun ce 'yan bindigar sun yi amfani da manyan makamai na zamani

Jami'an tsaro a Najeriya sun ce akalla mutane 22 aka kashe, a lokacin da wasu 'yan bindiga akan babura, suka afkawa Kauyen Mai tsaba a jihar Zamfara.

An kashe mutane 14 a garin mai tsaba, yayin da aka kashe mutane 8 na birnin tsaba da suka kai dauki.

Yawancin wadanda aka kashe 'yan banga ne dake kokarin kare kauyen daga mahara, kuma suna amfani ne da kayan fada na gargajiya.

Maharan sun dauki tsawon sa'a guda suna cin karensu ba babbaka, inda suka kona gidaje da dama a harin da ake ganin na ramuwar gayya ne.

Irin wadannan hare-haren sun kwashe shekaru suna faruwa a kauyukan Zamfara, kuma a kan dora alhakinsu ne kan Fulani dake zaune a dazuzzukan dake yankin.