Ebola: An kai hari akan ma'aikatan jinya

Hakkin mallakar hoto AFP

Rohotanni daga kasar Guinea na cewa an kai hari akan masu aikin jinya dake yunkurin dakile cutar Ebola.

Hukumomin kasar sun ce lamarin ya farune a garin Macenta dake kudancin kasar, bayan jita-jitar da aka yada ta cewa masu aikin jinyar ne, na kungiyar Medicins Sans Frontieres, MSF, suka kawo cutar.

Sai dai gwamnatin kasar ta jinjinawa MFR din, tana mai cewa badan namijin kokarinta ba, da Ebola ta zama ruwan dare a kasar.

Kimanin mutane 90 ne cutar ta hallaka a kasar ta Guinea da kuma Laberia

Karin bayani