Faransa ta samu sabani da Rwanda

Shugaban Rwanda Paul Kagame Hakkin mallakar hoto AP

Wata sa-in-sar diploamsiyya tsakanin Faransa da Rwanda ta kara kamari, yayinda hukumomin Rwandar ke shirin gudanar da bukuwan cika shekaru 20 da kisan kiyashin da aka yi a kasar inda aka hallaka mutane kimanin dubu dari takwas.

Ministan harkokin wanjen Rwanda, ya yi Allah wadai da shawarar da Faransa ta yanke ta kauracewa bukukuwan.

A jiya Asabar ne Faransa tace bazata halarci bukuwan ba saboda shugaba Paul Kagame ya zarge ta da hannu a kisan Tutsi da kuma 'yan hutu masu sassaucin ra'ayi.

Wani dan majalisar dokokin Faransar ya zargi shugaba Kagame da kokarin dauke hankalin duniya daga shi nashi laifukan