An kashe mutane 17 a Yobe

Hakkin mallakar hoto

Rahotanni daga Jihar Yobe da ke arewacin Najeriya sun ce an kashe akalla mutane 17 a wani hari da 'yan bindiga su ka kai a wani masallaci dake kauyen Buni Gari.

Rahotanni sun ce 'yan bindigar sun bude wuta ne a lokacin da jama'a ke sallar asuba a kauyen wanda ke da nisan kilomita 100 daga Damaturu babban birnin Jihar ta Yobe.

Yankin dai ya sha samun hare-hare wadanda ake dangatawa da 'yan Boko Haram.