An fara kada kuri'a a Afghanistan

Jaki dauke da akwatin da katunan zabe a yankin Panjshir na Afghanistan inda mota ba ta iya isa wajen Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan takara takwas ne dai suka fito domin maye gurbin Shugaba Hamid Karzai

Masu kada kuri'a sun fara jerin gwano a runfunan zabe a kasar Afghanistan domin zabar sabon shugaban kasa.

An tsaurara matakan tsaro a duk fadin kasar domin kare barazanar wargaza zaben da 'yan kungiyar Taliban suka ci alwashi.

Wannan shi ne zabe na farko da gwamnatin farar hula za ta mika mulki ga wata gwamnatin farar hular.

Wakilin BBC yace duk da hadarin da ke cikin zaben 'yan Afghanistan su na kokarin ganin sun kada kuri'arsu.

kuma mutane da dama da ba a taba ganin su ba sun fito an dama da su a yakin neman zaben.

Dubban jami'an tsaron Afghanistan ne ke samar da tsaro ga zaben, aikin tsaron da ake ganin shi ne mafi girma tun bayan hambarar da 'yan Taliban daga karagar mulki shekaru 13 da suka gabata.