Ghana na gwaji kan cutar Ebola

Accra babban birnin kasar Ghana
Image caption Accra babban birnin kasar Ghana

Hukumomin lafiya a Ghana na gwajin jinin wata yarinya 'yar shekaru goma sha biyu, wacce ta mutu sanadiyyar zazzabi da zubar jini.

Ana dai fargabar cewa zai iya zama cutar Ebola ta farko a kasar.

Shugaban sashen kula da lafiyar al'umma na asibitin koyarwa da ke Accra, babban birnin Ghana, Dennis Laryea ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa an debo samfurin jinin yarinyar ne daga babban asibitin Kumasi.

Fiye da mutane casa'in ne dai suka mutu sanadiyyar zazzabin Ebola a kasashen Guinea da Liberia, kuma an samu bayanin bullar cutar a kasar Mali.

Kungiyar ba da agajin lafiya ta Medicins sans Frontiers ta yi gargadin cewa akwai yiwuwar barkewar annobar Ebola a yankin Yammacin Afrika mai fama da raunin kiwon lafiya.