Nakasassu sun koka kan matsalar tsaro

Wasu wadanda aka kaima hari a asibiti Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wasu wadanda aka kaima hari a asibiti

Yayinda matsalar tabarbarewar tsaro ta ki ci ta ki cinyewa a Nijeriya musamnman a a rewacin kasar, ga alama su ma daidaikun jama'ar kasa da suka hada da nakasassu, lamarin ya dame su kuma ya na ci musu tuwo a kwarya.

Kan irin wannan damuwar ne nakasassu daga sassa dabam-dabam na jihar Bauchi dake arewa maso gabashin Nijeriyar, suka hallara a birnin Bauchi inda suka gudanar da addu'o'i na musamman tare da gabatar da kuka ga mahukuntan kasar kan yadda za a magance matsalar ta tsaro.

Malam Alhassan Tata Gurgu, Sakataren Majalisar Sarakunan nakasassu a jihar Bauchi, ya ce, adalci shine kawai hanyar da gwamnati za ta bi a harkokin mulki wajen kawo karshen matsalar rashin tsaro a Nijeriya.

Karin bayani