Matakan kariya daga Ebola a Nigeria

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Cutar Ebola na da saurin yaduwa tare da saurin kisa.

Kungiyar likitoci ta Nigeria ta bukaci hukumomin kasar su kula da kan iyakoki da kyau domin hana cutar Ebola bulla a kasar.

Shugaban kungiayar, Dr Osahon Enabulele ya shaida wa BBC cewa kamata ya yi a horar da jami'an shige da fice kan yadda za su tantance masu dauke da cutar Ebola.

Ya ce duk wanda ke da alamar zazzabi bai kamata a bar shi ya shiga Nigeria ba har sai an tabbatar da cewa ba cutar Ebola ba ce.

Cutar ta Ebola dai ta kashe akalla mutane 70 a Guinea da Liberia, ta kuma bulla a Mali, kuma ana zargin bullarta a Ghana.

Karin bayani