Ana ci gaba da zaman makoki a Zamfara

Image caption Har yanzu ana neman gawarwakin wasu daga cikin 'yan kauyen

Ana ci gaba da zaman makoki a jihar Zamfara dake arewacin Nigeria, bayan da wasu 'yan bindiga suka kashe mutane 120 a kauyen 'Yar Galadima.

Lamarin ya auku ne a ranar Asabar inda inda 'yan bindiga wadanda ake zargin Fulani ne suka kai hari a kauyen lokacin da 'yan banga da kuma manoma ke taro a kan yadda za su bullo ma hare-haren da ake kai musu.

A ranar Lahadi aka yi jana'izar wadanda suka rasu, a yayinda wasu mazauna kauyen ke cewar adadin wadanda suka rasu ya kai 150.

Hankalin jama'a a daukacin jihar ya tashi sakamakon wadannan kashe-kashen kuma a halin yanzu jami'an tsaro sun ce sun soma bincike don gano 'yan bindigar.

Gwamnan Jihar Zamfara, AbdulAzeez Yari wanda ya jajantama 'yan uwan wadanda aka kashe, ya ce an yi taron 'yan bangar da manoma ba tare da izini ba.

'Yan bindiga da ake zargi Fulani ne sun kaddamar da hare-hare a watan daya wuce a jihar Katsina inda suka kashe mutane fiye da 100.

Karin bayani