Al-Shabab: An damke mutane 400 a Kenya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jami'an tsaro a Kenya suna sintiri a Eastleigh

Hukumomi a Kenya sun ce sun tsare mutane fiye da 400 a samamen da suka kai a kokarin tabbatar da tsaro a cikin kasar.

An tsare mutanen ne bayan harin gurneti da aka kai a makon da ya wuce a lardin Eastleigh inda galibin al'ummar Somalia ke zaune a birnin Nairobi.

Galibin wadanda aka tsare din 'yan Somalia ne.

Yawancinsu an tsare su, na tsawon kwanaki uku a wani filin wasa a Nairobi.

Kungiyoyi kare hakkin bil adama na Majalisar Dinkin Duniya da kuma 'yan uwan mutanen sun ce kawo yanzu an hanasu ganawa da wadanda aka tsaren.

Ministan harkokin cikin gida a Kenya, Joseph Ole Lenku ya ce wadanda aka tsare ba suda takardun izinin shiga kasar, za a tasa keyarsu zuwa Somalia.

Karin bayani