NATO ta gargadi Rasha a kan Ukraine

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Anders Fogh Rasmussen

Kungiyar tsaron NATO ta gargadi Rasha da cewa, za ta yi kuskuren da bata taba yi ba a tarihi, idan har ta sake tsoma baki a Ukraine.

A cewar NATO yin hakan zai haddasa mummunan tasiri, wanda zai sa Rashar ta kara zama saniyar ware.

Sakataren Kungiyar Anders Fogh Rasmussen ya kuma bukaci Rasha ta soma janye dubban dakarunta daga kan iyakarta da Ukraine kuma ta soma tattaunawar sulhu da hukumomi a Kiev

A nata bangaren, Rasha ta yi kashedin cewa, duk wani mataki na murkushe masu zanga-zangar nuna goyon bayanta a gabashin Ukraine, zai iya janyo yakin basasa.

Karin bayani