Dokar takaita haihuwa a Philippines

Image caption 'Yan Roman Katolika sun nuna rashin amincewa

Kotun kolin Philippines ta amince da dokar takaita yawan 'ya 'yan da kowanne dan kasar zai iya haifa.

Ana kallon wannan hukuncin tamkar shan kaye ne ga matsayin cocin Roman Katolika na Kiristoci.

Cocin Roman Katolika na adawa da wannan matsayin na takaita yawan iyali.

Dokar ta bukaci cibiyoyin kiwon lafiya na gwamnati su raba kwaroron roba kyauta, da kuma magungunan tsara iyali.

Kasar Philippines na da yawan jama'ar da suka kai miliyan dari, kuma na cikin kasashen da suka fi yawan hayayyafa a duniya.

Karin bayani