Pistorius: An dage zaman kotu saboda kuka

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Oscar ya musanta kisan budurwarsa da niyya

An dage shari'ar zakaran tseren nan, Oscar Pistorius zuwa ranar Laraba, bayan dan Afrika ta Kudun ya kasa cigaba da ba da bahasi yana ta kuka.

Oscar ya dinga shisshika a lokacin da ya ke bayanin abin da ya faru, a dare da ya harbe budurwarsa Reeva Steenkamp.

Mr. Pistorius ya ce ya dauki bindigarsa, saboda ya yi tsammanin wani ne ya shiga gidansa, kuma bayan ya ji motsi a bandaki sai ya harbi kofar bandakin sau hudu.

Ya ce ya yi ta kururuwa, sannan ya fasa kofar bandakin da sandar kurket, inda ya sami Reeva a ciki.