An kashe mutane da dama a Taraba

Hakkin mallakar hoto google
Image caption An tura karin jami'an tsaro a Jubu

Rahotanni daga jihar Taraba dake arewa maso gabashin Nigeria na cewa mutane da dama sun rasa rayukansu a sakamakon wani hari da wasu masu dauke da muggan makamai suka kai a garin Jubu na karamar hukumar Wukari.

Mazauna garin sun shaidawa BBC cewar adadin mamatan ya kai kimanin ashirin a harin da aka kaddamar a safiyar ranar Talata.

Hukumomin jihar ta Taraba sun tura karin jami'an tsaro zuwa yankin, amma dai rahotanni na cewa tuni kura ta lafa koda yake ana ci gaba da zaman dar-dar.

Wani mazaunin garin ya bayyana cewar maharan sun kona gidaje da wasu gine-gine a garin baya ga kashe akalla mutane biyar, amma su ma maharan an kashe kimanin goma sha biyar daga cikinsu.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar ta Taraba, DSP Joseph Kwaji, ya tabbatar da afkuwar lamarin amma ya ce ba zai iya tabbatar da hasarar rayuka ba kana ya musanta zargin cewa akasarin jami'an tsaro sun gudu.

DSP Kwaji kuma ya danganta rigimar da bazuwar tashin hankali tsakanin Fulani da Tibi a jihohin Benue da Nasarawa masu makwabtaka da Taraba.

Wannan lamarin na Wukari na zuwa ne yayin da jama'ar yankin Ibi duk a jihar ta Taraba ke ci gaba da kokawa kan mummunan tasiri da dokar hana fita ba dare ba rana da mahukunta suka kafa a yankin tun ranar Asabar da ta gabata sakamakon wasu kashe-kashe da aka fuskanta.

Karin bayani