BBC Hausa Facebook ya yi goshi

Image caption Muna godiya ga dumbin masu sauraronmu da bin mu a shafukan sada zumunta, musamman BBC Hausa Facebook

A daren ranar Talata ne masu bibiyar shafin BBC Hausa Facebook su kai mutane 500,000.

Shafin da ke kawo wa masu shiga ciki labarai da bayanai daga BBC Hausa, ya zamo wani dandali na muhawara da kuma sada zumunta ga dimbin masu sauraronmu tun farkon bude shi.

A watan Janairun shekarar 2010 ne dai muka bude shafin na BBC Hausa Facebook, dankon zumuntan da muke fatan zai fi haka karfi.

Domin haka muna fata za ku ci gaba da bibiyar shafin tare da gaiyatar 'yan uwa da abokan arziki, su kasance tare da BBC Hausa Facebook.