An kashe 'yan sanda bakwai a Jigawa

Hakkin mallakar hoto Getty images
Image caption Yankin arewacin Nigeria ya kwashe shekaru yana fama da hare-haren Boko Haram

Rundunar 'yan sandan jihar Jigawa ta tabbatar da kisan jami'anta bakwai, a wani hari da ake zargin 'yan Boko Haram da kai wa.

Rundunar ta kuma ce an jikkata wani jami'inta daya, a harin da aka kai wa caji ofis dinta na Gwaram, a ranar Talata da daddare.

Sai dai wasu mazauna garin na cewa, 'yan sandan da aka kashe a harin sun kai tara.

Ko da yake jihar ta Jigawa na makotaka da jihar Yobe, daya daga cikin jihohi uku dake karkashin dokar ta baci, ba kasafai 'yan kungiyar ta Boko Haram ke kai mata hari ba.