An ceto bakin haure 4,000 a Italiya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Bakin haure masu kokarin tsallakawa kasar Italiya

Hukumomin Italiya sun ce, cikin sa'oi arba'in da takwas da suka gabata sun ceto bakin haure dubu hudu dake cikin wani jirgin ruwa a tekun Mediterranean.

Ministan harkokin cikin gida, Angelino Alfano ya ce, lamarin bakin haure da dake kokarin tsallakawa Turai yana kara zama wata babbar matsala.

Ministan ya kuma yi kira ga kasashen kungiyar tarayyar Turai su matsa kaimi wajen kawo karshen abinda ya kira, kasuwanci da rayukan jama'a.

A cikin watan Oktoban bara, bakin haure 'yan Eriteria su dari uku da sittin ne jirgin ruwa ya kife da su.

Karin bayani