Nigeria:'Kowace jiha ta ci arzikinta'

Image caption Lamidon Adamawa ya kuma ce sarakuna ba sa bukatar matsayi a kundin tsarin mulkin kasar

Daya daga cikin sarakunan arewacin Najeriya da ke halartar taron kasa ya bukaci da a bai wa jihohin da ke da arzikin mai damar mallakar kudaden man dari bisa dari.

Lamidon Adamawa, Alhaji Barkindo Aliyu Mustafa ya kuma bukaci su ma jihohin da ba su da arzikin man, a ba su damar rike arzikin da suke da.

Ya ce tun da wasu sun bar ainihin batun da ya sa aka kira taron sun fara kiran a basu damar iko da arzikinsu, to shi ma zai bukaci a soke iznin mallakar filaye daga wadanda ba 'yan arewa ba a Abuja da wasu sassan Arewa, ta yadda za su rika biyan kudin haya ga jihojin arewa kan gine-ginen da suka yi a filayen.

Ko a kwanakkin baya ma wasu kalamai da basaraken ya yi a wajen taron sun jawo ka-ce-na-ce.

Karin bayani