Jirgin Malaysia: An ji sabon sauti

Hakkin mallakar hoto
Image caption Sojan ruwan Amurka ma sun jiyo wasu sautukan biyu su ma da suka yi daidai da na na'urar.

Jagoran 'yan Australiya masu aikin binciken jirgin saman Malaysia da ya yi batan dabo ya ce an sake jin wasu sautuka biyu cikin teku wadanda mai yiwuwa ne sun fito daga na'urar nadar bayanan jirgin ne.

A cewar Shugaban na hukumar da ke tsara aikin neman jirgin ta kasar Australiya, Angus Houston, an ji amo na farko ranar Talata da rana kuma ya dauki tsawon mintuna 5 da dakika 25 ana jinsa, yayin da aka ji na 2 da daren Talatar kuma ya dauki mintuna 7 ana jinsa.

''Ya ce na yi imanin muna binciken ne a yankin da jirgin nan yake. Amma muna bukatar mu ga tarkacen jirgin kafin mu tabbatar da cewa nan ne jirgin na MH 370 ya fada.

Houston ya ce jin wadannan sautukan zai ba jami'ai damar mai da karfin binciken a wannan yankin inda za a iya tura wata mota mai tafiya karkashin teku mai suna Bluefin-21 wadda ke cikin katafaren jirgin ruwan Rundunar Sojan Ruwan Australiya da ke laluben jirgin wato Ocean Shield, zuwa kasan tekun domin ta nemo tarkacen jirgin.

Karin bayani