Cutar Ebola na yi wa Nigeria barazana

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Cutar ta soma barkewa ne a kasar Guinea

Gwamnatin Nigeria ta ce kasar na fuskantar barazana daga cutar Ebola wacce a yanzu ke yaduwa a kasashen yammacin Afrika.

Ministan kiwon lafiya na kasar, Farfesa Onyebuchi Chukwu ya ce duk da cewar babu cutar a Nigeria, amma dai akwai bukatar mutane su farga a kan illa cutar don kaucewa barkewarta a cikin kasar.

A cewar Ministan, cutar ta riga ta bulla a kasashen dake makwabtaka da Nigeria kuma kawo yanzu babu maganinta ko kuma allurar rigakafinta.

Farfesa Chukwu ya ce cibiyar kula da cuttuka ta kasar za ta soma yekuwa a kafafen yada labarai domin a wayar wa da 'yan Nigeria kai game da cutar da illolinta da kuma yadda ake iya kamuwa da ita.

A halin yanzu dai cutar Ebola ta kashe fiye da mutane 100 a kasar Guinea, kuma ta bulla a kasashen Liberia da Saliyo da kuma Mali.

Karin bayani