Taron Kasa: shakku kan kuri'ar raba-gardama

Image caption Wakilan dai sun kwashe makonni biyu yanzu suna muhawara kan jawabin shugaban kasar.

Wasu daga cikin wakilan taron kasar da ake gudanarwa a Nigeria na bayyana shakku game da yiwuwar gudanar da kuri'ar raba-gardama kan shawarwarin da za'a fitar a karshen taron.

Wannan na zuwa ne yayin da wakilan ke ci gaba da yin tsokaci dangane da irin abubuwa da ke kunshe a cikin jawabin da Shugaba Goodluck Jonathan ya yi wa wakilan a ranar da aka kaddamar da babban Taron; inda ya ce idan ta kama za a iya yin kuri'ar raba-gardama kan shawarwarin da taron ya cimma.

''Ana maganar yin kuri'ar raba-gardama ne in akwai gardamar e ko a'a. Amma idan kana maganar abu kamar kundin tsarin mulki da ke abubuwa daban-daban sun fi 400 a ciki, yaya za a yi ka yi kuri'ar raba-gardama? '' Inji daya daga cikin wakilan masu wannan ra'ayin AVM Mukhtar Muhammed.

''Abubuwa wajen guda 25 ne aka shimfida. Yaya za a yi a gabatar da abubuwa 25 ga talakawa su jefa kuri'a a kai? Me suka sani game da tsarin shugaba mai cikakken iko ko na Firai minista irin na Burtaniya? '' Muhammad Sani Zoro shi ma wani wakilin ya tambaya.

Karin bayani