An kai hari gidan kallon kwallo a Yobe

Image caption Wasu na zargin 'yan Boko Haram da kai harin

Rundunar 'yan sandar jihar Yobe a Nigeria ta ce wani mutum ya mutu, kuma wasu shida suka jikkata, a lokacin da wasu 'yan bindiga suka kai hari gidan kallon kwallo.

Lamarin ya faru ne a daren ranar Laraba, a lokacin da gidan kallon dake kasuwar 'yan katako a Potiskum ya cika makil, inda mutane ke kallon wasanin Manchester United da Bayern Munich da Atlentico Madrid da Barcelona.

Wani wanda ya shaida lamarin ya ce maharan su uku sanye da kayan soji, sun bude wa masu kallon wuta.

Sai dai kwamishinan 'yan sandar jihar, Sanusi Rufa'i yace ba sojoji ba ne suka kai harin.