Mai amfani da twitter ya yi batan dabo

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wurin da yake aiki dai na makwabtaka ne da hedikwatar hukumar ta SSS.

Hukumar kare hakkin dan adam ta Najeriya ta ce tana wani bincike game da bacewar wani amfani da shafin Twitter da aka daina gani tun kwananakki 10 da suka wuce.

Yusuf Isiyaka ya bace ne ranar da aka yi musayar wuta tsakanin jami'an tsaro masu farin kaya watau SSS da wasu mutane da hukumar ta SSS ta ce 'yan kungiyar Boko Haram ne dake kokarin tserewa; inda mutane 18 suka halaka.

Mutumin wanda ke aiki a tashar ba da wutar lantarki da ke cikin fadar shugaban kasa da ke makwabatar da hedikwatar hukumar, ya shaidi abin da ya afku a hedikwatar ta SSS kuma ya aike da hotunan lamarin ta shafinsa na Twitter.

'' A ranar 30 watan Maris lokacin da aka yi musayar wuta a hedikwatar ta SSS, Yusuf Isiyaka yana aiki; kuma ya matsa kusa ya dauki hotunan abin ke faruwa ya kuma aike da su kai tsaye ta shafin twitter'' Inji Abba Mohammed wani wakilin BBC a Abuja.

Karin bayani