Samsung ya kaddamar da Galaxy S5

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wayar Galaxy S5

Kamfanin Samsung ya kaddamar da sabuwar waya Galaxy S5 don ci gaba da hamayya da kamfanin Apple.

Wayar Galaxy S5 wacce ruwa baya yi wa lahani an yi mata ado fiye da Galaxy S4 wacce kamfanin ya fitar a bara.

Galaxy S5 na daukar hoto rangadau sannan batirinta na dadewa.

Kamfanin kasar Koriya ta Kudu ne ke kera wayar Samsung, kuma ya fitar da wasu sabbin agogon hannu na komai da ruwanka.

Babban kamfanin da ke goggawa da Samsung wato Apple shi ma nan gaba kadan zai kaddamar da wayar iPhone 6.

Kamfanoni irinsu Nokia, Blackberry da HTC duk suma sun kera wayoyin komai da ruwanka.

Karin bayani