An kashe mutane 130 a Jihar Borno

Hakkin mallakar hoto AFP

Rahotanni daga Jihar Borno, a arewacin Najeriya, sun ce wasu 'yan bindiga da ake kyautata zaton 'yan kungiyar Boko Haram ne sun kashe fiye da mutane 130 a hare-haren da su ka kai a sassa daban daban na jihar.

'Yan bindigar sun kai hare-haren ne a yankunan Dikwa da Kala-Balge da kuma kauyen Dalwa a ranakun Alhamis da Juma'a.

Mazauna yankunan sun ce 'yan bindigar sun harbe mutane da dama da bindiga, sa'annan su ka kona wasu wuraren.

Sun ce jami'an tsaro ba su kai dauki ba, duk da cewa an sanar da su.

Sanata Ahmad Zannah, mai wakiltar yankin a Majalisar Dattawan Najeriya, ya ce rahotannin da ya samu sun nuna cewa an kashe kimanin mutane 130 zuwa 200 a sabilin wadannan hare-haren.

Ya ce jama'ar yankin, musamman ma yara da mata, na cikin wahala sosai.

Wani daga cikin mazauna yankin ya ce mutane da dama sun tsere zuwa Jamhuriyar Kamaru, mai makwabtaka da Najeriyar.

Jami'an tsaron Najeriyar ba su ce komai ba game da lamarin.

Karin bayani