Rahoton MDD kan dumamar Duniya

Ban ki Moon Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Matsalar dumamar yanayi dai na ci gaba da zama kalubale a duniya.

A yau da safiyar nan ne Masana kimiyya daga Kwamitin kwararru kan Nazarin sauyin yanayi na Majalisar Dinkin Duniya za su fitar da sabon rahotonsu kan yadda za a tunkari matsalar dumamar duniya.

Ana sa ran rahoton zai yi kiran a yi sauyi da gaggawa daga amfani da makamashi mai fitar da hayaki kamar su kwal zuwa makamashi wanda bai samar da hayaki.

Wanda kuma ake iya sake sarrafawa; domin rage sakin gurbataccen iskan Carbon cikin sararin samaniya.

Akwai yiwuwar kwamitin na IPCC yayi kiran a ninka samarda sabbin hanyoyin samun makamashi kamar masu amfani da hasken rana ko Iska.

Karin bayani