Zabe a Guinea Bissau

Shugaban rikon kwarya na Guinea Bissau Manuel Serifo Nhamadjo Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kasar dai ta sha fama da juyin mulki a lokuta daban-daban.

A yau ne za a fara gudanar da zabukan shugaban kasa da 'yan majalisu a 'yar karamar kasa da ke yammacin Africa wato Guinea Bissau.

Wannan dai shi ne zabe na farko da za a gudanar a kasar tun bayan wani juyin mulki da aka yi shekaru biyu da suka gabata, wanda shi ne juyin mulki na karshe da sojoji suka yi.

Da ya tattabar da babu wani zababben shugaban kasa da ya kammala wa'adin mulkinsa a kasar tun bayan karbar yancin kai daga Portugal a shekarar alif dari tara da saba'in da hudu.

Jagoran juyin mulkin Antonio Indjai ya mika mulki ga gwamnatin rikon kwarya ta farar hula a shekarar dubu biyu da sha biyu domin fara shirye-shiryen wannan zabe.

Ana dai tsare da shi a Amurka inda ake tuhumarsa da safarar miyagun kwayoyi da saidawa 'yan tawayen Colombia makamai.

Mutane goma sha uku ne dai suka tsaya takarar shugabancin kasar, kuma idan ba wanda ya lashe mafi yawan kuri'un to za a sake gudanar da zagaye na biyu na zaben a watan gobe.