Ebola: An hana mutane shiga Gambia

Hakkin mallakar hoto AFP

Jami'ai a kasar Gambia sun sanar da komfanonin jiragen sama cewa kada su dauki fasinjoji daga kasashen Guinea da Liberia da Sierra Leone zuwa kasar su saboda gudun yada cutar Ebola.

Da yake magana akan sanarwar, ministan harkokin wajen Sierra Leone Samoura Kamara yace Gambiyar nada ikon tsare kasar ta da jama'ar ta.

Senegal ma ta rufe iyakar ta da Guinea saboda tsoron cutar Ebola.

Fiye da mutane dari ne cutar ta hallaka a Guinea da Liberia