Mai amfanin da Twitter da ya bace ya dawo

Image caption Mutane ashirin da daya ne suka mutu cikin musayar wutar da faru lokacin da wasu tsararru suka so tserewa.

An sako wani mutum dan Najeriya da aka kama bayan aike wa da hotunan musayar wutar da aka yi a Hedikwatar 'yan sandan ciki a Abuja, bayan kwashe kusan makonni biyu a tsare.

Yusuf Isiaka ya yi batan dabo ne a watan jiya jim kadan bayan aika hotunnan harbe-harben ta shafinsa na twitter.

Dan uwansa Sanusi Onimisi ya tabbatar da sako mutumin dan shekaru 32, sai dai har yanzu mutumin bai ce komai ba.

'' Na yi magana da shi yau (assabar) kuma mamarmu tana can tare da shi a Abuja'' Inji Sanusi Onimisi Isiaka a wata hira da kamfanin dillacin labarai na AFP ; ya kara da cewa '' Na gode wa dukkan 'yan Najeriya da kafafen watsa labarai da kuma kungiyoyin kare hakkin dan adam na ciki da waje da suka yi tsayiN daka waje ganin a sako dan uwana.''

Karin bayani