Bom ya hallaka mutane 71 a Nyanya Abuja

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan kwana-kwana sun kai dauki

Mutane akalla saba'in da daya sun rasu sakamakon tagwayen abubuwa da suka fashe a wata tashar mota a Nyanya da ke Abuja babban birnin Nigeria.

Shugaban hukumar agajin gaggawa ta Abuja, Abbas Idris wanda ya tabbatarwa da BBC wannan adadin, ya ce kuma wasu mutane 124 sun samu raunuka sakamakon harin bom din a Nyanya.

Kakakin rundunar 'yan sandan Nigeria, Frank Mba ya ce tashin bam din ya rutsa da manyan motoci 16 da kuma kananan motoci 24.

Abubuwan sun fashe ne a lokacin da mutane ke kokarin shiga mota don zuwa aiki a cikin garin Abuja.

Shaidu sun bayyana cewar sun ga gawarwaki warwatse a yankin.

Ana zargin 'yan Boko Haram ne suka kai karin.

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Tashar motar Nyanya na da cinkoson jama'a

Wani mutumi Badamasi Nyanya ya shaidawa BBC cewar ya ga gawarwaki kusan 40.

Wakilin BBC Haruna Shehu Tangaza wanda ya ziyarci asibitin Maitama da ke Abuja, ya ce mutane da dama sun samu raunuka kuma suna samun kullawar gaggawa.

'Kara Mai Karfi'

Wata ma'aikaciya Mimi Daniel wacce ke aiki a cikin garin Abuja ta ce "Ina jiran mota lokacin dana ji kara mai karfi sannan sai hayaki ya turnuke wajen".

Mutane dai a kusa da tashar ta Nyanya sun kidime inda kowa ya yi ta kansa.

A bana 'yan Boko Haram sun kashe mutane fiye da 1,500 a jihohi uku da ke arewa maso gabashin Nigeria.

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption A bana 'yan Boko Haram sun kashe mutane 1,500

Kungiyar Boko Haram ta sha kai hare-hare a Abuja, ciki hadda a ofishin Majalisar Dinkin Duniya a shekara ta 2011.

Wannan harin cikas ne ga Shugaba Goodluck Jonathan a kokarinsa na tabbatar da tsaro a cikin kasar.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Taswirar Abuja

Shugaban kuma ya bayyana takaicinsa game da abinda ya faru a Nyanya inda ya bada umurnin a tsaurara matakan tsaro a Abuja babban birnin kasar.

Karin bayani