Binciken masu kishin Islama a Ingila

Image caption Wasu makarantu a Birmingham

An soma bincike a Ingila bisa zargin cewar masu tsananin kishin Islama na kokarin kwace makarantu a garin Birmingham, inda a yanzu aka soma binciken makarantu 25.

Karamar hukumar Birmingham ta ce ta samu takardunkun koke 200 game da wannan zargin.

Mutane sun yi zargin cewar Musulmai na kokarin kwace ikon gudanarwar makarantu a birni.

Kawo yanzu an soma bincike kan makarantu 25 ciki hadda na Faramare da Sakandare.

Iyayen yara da malaman makaranta na daga cikin wadanda suka yi korafin.

'Fadada Bincike'

Mr Ian Kershaw wanda shi ne ke lura da harkokin Ilimi a arewacin Ingila, ya ce zai gudanar da bincike tare da nazari kan korafe-korafen da aka gabatar.

Yace zai yi aiki ne tare da kansiloli da 'yan sanda da 'yan majalisar dokoki da kuma kungiyoyin addinnai.

A bara dai an yi zargin cewar hukumomi sun kori shugabannin makarantu hudu saboda kawo tsatsaurar akidar addinnin musulunci a cikin harkokin makaranta.

A yanzu dai ana fadada bincike kan wannan batun a wasu birane kamarsu Manchester da Bradford.

Sir Albert ya ce "Akwai batutuwa a Bradford masu kama da irin na Birmingham".

Karin bayani