Nyanya: Jonathan ya bayyana takaici

Hakkin mallakar hoto reuben abati
Image caption Shugaba Jonathan ya kai ziyarar gani da ido a wurin

Shugaban Nigeria, Goodluck Ebele Jonathan ya bayyana takaicinsa game da abinda ya faru a Nyanya, inda mutane da dama suka rasu.

Kakakin Shugaban kasar, wato Dr Reuben Abati ya bayyana cewar shugaban ya bada umurnin a tsaurara matakan tsaro a Abuja babban birnin kasar.

Shugaba Jonathan kuma ya mika ta'aziyarsa ga iyalan wadanda suka rasa 'yan uwansu sakamakon fashewar bam din.

Ya kuma bukaci jami'an kiwon lafiya su bada kulawar gaggawa ga wadanda lamarin ya rutsa dasu.