Ana ci gaba da bore a gabashin Ukraine

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Masu zanga-zanga a Ukraine

Masu goyon bayan Rasha sun kai hari a wani ginin gwamnati a gabashin Ukraine sannan suka lalata wani caji ofis a birnin Horlivka.

'Yan tada kayar baya sun ci gaba da kwace gine-ginen gwamnati a wasu birane bayan kin bin umurnin gwamnati nasu fice daga gine-ginen ko kuma dakarun Ukraine su fitar dasu.

A Moscow, Ministan harkokin wajen Rasha, Sergie Lavrov ya karyata zargin cewar na da hannu a lamarin dake faruwa a lardin.

A cewarsa, Rasha bata son kasar Ukraine ta ruguje.

Mr Lavrov ya kuma zargi kasashen yammacin duniya da yin munafirci na kokarin hana zanga-zanga a gabashin Ukraine.

Karin bayani