Berlusconi zai yi aiki a gidan tsofaffi

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Silvio Berlusconi

An umurci tsohon Firaministan Italiya, Silvio Berlusconi, yayi aiki a wani gidan tsofaffi akalla sau daya a mako, a madadin hukuncin daurin shekara dayar da aka yanke masa.

Kotu ta same shi da laifin kin biyan haraji.

Kotun kolin Italiyar ce ta yanke masu hukuncin daurin, to amma saboda shekarunsa, sai aka ce ko dai a yi masa daurin talala, ko kuma yayi wani aiki na taimakon al'umma.

Wakilin BBC a birnin Rome ya ce, Silvio Berlusconi, mai shekaru saba'in da bakwai a duniya, zai ji takaicin wannan hukuncin ainun.

To sai dai kuma a cewar wakilin BBC din, ba a san ma ko tsofaffin za su yi maraba da Berlusconi ba ko kuma a'a.

Karin bayani