Shin 'yan Boko Haram sun gagara ne?

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dakarun tsaro na sintiri a jihar Borno

Abisa dukkan alamu ayyukan 'yan kungiyar Boko Haram a wannan shekarar sun nuna cewar kungiyar na matukar barna a sassa daban daban na Nigeria.

Alkaluman da aka fitar a hukumance sun nuna cewar rikicin 'yan Boko Haram ya shafi mutane kusan miliyan uku a jihohin arewa maso gabashin Nigeria.

Haka kuma mutane fiye da dubu 250 sun rasa muhallansu sakamakon ayyukan 'yan Boko Haram.

Tun daga farkon wannan shekarar rayukan mutane fiye da 1,800 suka salwanta sakamakon hare haren 'yan kungiyar.

Hakkin mallakar hoto NEMA
Image caption Mata da kananan yara sun shiga mummunan hali

Kusan shekara guda kenan da Shugaban Nigeria, Goodluck Jonathan ya kafa dokar ta-baci a jihohin Adamawa da Borno da Yobe a yunkurin kawo karshen zubar da jini a yankin, amma kawo yanzu a iya cewa lamarin na kara muni ne saboda dimbin rayukan da aka kashe.

Wani Malami a Jami'ar Modibbo Adama ta Yola, Farfesa Kyari Muhammed ya bayyana cewar gwamnati ta gaza, don haka akwai bukatar jami'an tsaro su sauya salon yadda su ke tunkarar 'yan Boko Haram idan suna son kawo karshen tashin hankalin.

'Sace Dalibai'

A ranar Litinin aka sace dalibai mata 'yan sakandaren kwana ta garin Chibok a jihar Borno, bayan da 'yan bindiga da ake zargin 'yan Boko Haram ne suka ci karfin jami'an tsaro sannan kuma suka kona gidaje kusan 100 a garin.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dalibai da dama a jihar Borno sun daina zuwa makaranta

Wasu daga cikin iyayen da BBC ta tattauna da su, sun bayyana cewar kawo yanzu ba su ji duriyar 'ya'yansu ba, kuma hakan ya jefa su cikin zullumi.

Daya daga cikin iyayen ya shaidawa BBC cewa hankalinsa zai fi kwanciya, idan da gawar 'yarsa ya gani, da wannan yanayi na bakin ciki da rashin tabbas da suka shiga.

Dakarun Nigeria sun ce sun bazama don gano inda 'yan matan suke, yayinda ake zaton 'yan Boko Haram din sun shiga da su cikin dajin Sambisa.

Sace 'yan matan a jihar Borno ya zo ne kwana guda bayan da aka kai hari a Nyanya a birnin Abuja, inda mutane kusan 75 suka rayukansu, sannan wasu karin 130 suka samu munanan raunuka.

A ranar da aka sace daliban kuma an kashe matafiya kusan 18 a garin Gwoza na jihar ta Borno.

'Gangamin PDP'

Duk da mummunan tashin hankalin da ke fuskantar Nigeria, Shugaba Goodluck Jonathan ya tafi birnin Ibadan don bukin taya basaraken gargajiya a garin murnar dadewarsa a kan karagar mulki.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Jonathan na yawon Kampe

Mr Jonathan kuma ya garzaya birnin Kano, inda ya yi bukin kabar tsohon gwamnan jihar, Ibrahim Shekarau zuwa PDP, lamarin da ya sa wasu ke caccakar shugaban a matsayin 'mara tausayi'.

Masu sharhin na ganin cewar abinda shugaban ya sa a gaba shi ne neman mulki ba abubuwan kare rayukan al'ummar kasar ba.

Sai dai ministan harkokin wajen Nijeriya, Ambasada Aminu Wali ya kare shugaban kasar yana cewa, ba rashin tausayi ba ne, yanayin da kasar ta shiga, tilas ne a rika cizawa ana busawa.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Hare-haren sun zama ruwan dare a Borno

Gwamnan Kano, Rabiu Kwankwanso ya ce ziyarar Shugaba Jonathan a Kano ta nuna cewar bai damu da mummunan halin da 'yan kasar suka shiga ba.

Game da wannan furuci wasu mukarraban Shugaban kasar sun ce maida wa Gwamna Kwankwaso martani, suna zarginsa da nuna adawa kawai.

Masu nazarin kan abubuwa a Nigeria na cewar dole ne sai gwamnati na nuna cewar da gaske take yi don kawo karshen zubar da jini a kasar, saboda a halin yanzu tamkar an bar 'yan Boko Haram suna cin karensu babu babbaka ne.

Karin bayani