Wata ya yi husufi a Amurka

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Husufin Wata a Amurka

Al'ummar yankin Amurka da Caribbean sun kalli wata na husufi, inda watan ya sauya kala ya koma ja.

Watan ya yi husufi na tsawon sa'o'i uku daga misalin karfe 05:58 agogon GMT na ranar Talata.

Bayan sa'o'i biyu sai watan ya soma koma wa launinsa na asali kafin ya wattsake.

Ana hasashen cewar za a yi husufin na wata sau hudu a shekara ta 2014.

Sannan a ranar 29 ga watan Afrilu rana ita ma za ta yi husufi.