Nyanya: APC da PDP na cacar baka

Shugaba Goodluck a Nyanya Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Goodluck a Nyanya

Babbar Jam'iyyar adawa ta APC ta nemi gwamnati ta kira babban taron kasa kan tabarbarewar sha'anin tsaro.

Sakataren watsa labarai na jam'iyyar Alhaji Lai Mohammed a wata sanarwa da ya bayar, ya ce, hare-haren da ake kaiwa cikin kasar babu kakkautawa ya nuna gazawar gwamnati.

To, amma mataimakin sakataren yada labarai,na jam'iyyar PDP Barrister Abdullahi Ibrahim Jallo ya ce, ba gwamnati ba ta gaza ba.

Jami'in na PDP ya ce, alhakin kula da tsaro ya rataya ga wuyan kowa, yana cewar wannan wani sabon abu ne, yana nuni da abubuwan dake faruwa a wasu kasashen duniya wurinda ake tashe-tashen hankula.

Harin da aka kai a ranar Litinin a Nyanya da ke birnin Abuja, ya janyo mutuwar mutane akalla 71 a yayinda fiye da 130 suka samu raunuka.

Karin bayani