Ana shan tsada wajen tura kudi zuwa Afrika

Image caption Kungiyoyi sun yi kira ya kamata a sauya tsarin

Wata cibiyar bincike da ke Birtaniya-Cibiyar Raya kasashen waje ta ce kudaden da ake biya wajen tura kudade zuwa nahiyar Afrika, ya fi na ko'ina tsada a duniya.

Cibiyar ta yi nazari ne kan aike wa da dala dari biyu, inda ta gano cewa ana karbar kashi sha biyu cikin dari na wannan adadi, a matsayin lada, adadin da kusan ya ninka wanda ake biya wajen tura kudade a sauran kasashe na duniya.

Cibiyar Raya kasashen wajen ta ce asarar da ake yi ta kai dala biliyan guda da miliyan dari takwas a duk shekara, a matsayin karin kudin da ake cazar jama'a, za a iya amfani da su wajen bayar da ilmi ga yara miliyan goma sha hudu.

Wannan hanya ta tura kudade gida, babbar hanya ce ta samun kudaden shiga ga kasashen Afrika na kudu da hamadar Sahara.

Bankin duniya ya bayyana cewa a 2013 , 'yan Afrika sun tura abin da ya kai dala biliyan 32 zuwa kasashensu, adadin da kusan ya kai na kudaden agajin da aka tura ma kasashen Afrikan.

Kamfanoni irinsu MoneyGram da Western Union, wadanda su ne gaba gaba da ake amfani da su wajen tura kudaden sun ce kudaden da suka caza sun dogara ne kan wasu dalilai masu dama.

Sun ce dabarun da suka bullo da su, sun baiwa masu aike wa da kudaden karin zabi na hanyoyin da zasu yi amfani da su.