Chibok: Sojoji na yunkurin ceto dalibai

Boko Haram Najeriya
Image caption Boko Haram Najeriya

Jami'an tsaron Najeriya na cigaba da neman wasu 'yan mata dari da ake zargin 'yan kungiyar Boko haram ne suka sace su a jihar Borno dake arewa maso gabashin kasar.

'Yan matan dai suna rubuta jarrabawar su ne.

Kakakin rundunar tsaron Nigeria, Manjo Janar Chris Olukolade ya bayyana cewar ana aiki tsakanin sojin kasa da na sama don gano dajin da aka kai 'yan matan.

Dan Majalisar Dattijjai a Nigeria, Sanata Muhammed Ali Ndume ya shaidawa BBC cewar an gano babbar motar da aka kwashi 'yan matan an yi watsi da ita, don haka ana zargin mutanen da suka sace su sun tasa-keyar su ne suna tafiya da su cikin daji.

Ko da yake wasu iyaye da BBC ta yi hira da su sun ce kawo yanzu basu ga 'ya'yansu ba, yayin da wasu 'yan matan kalilan suka samu kubucewa.

Jihar Borno ce matattarar kungiyar Boko Haram, inda suka kashe mutane fiye da 1,800 a wannan shekarar.

Hakan na zuwa ne bayan wani hari da aka kai Nyanya dake wajen garin Abuja, inda aka kashe mutane 72 tare da raunata mutane fiye da 130.