Ana cigaba da zaman dar-dar a Wukari

Tashin hankali a Najeriya Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Tashin hankali a Najeriya

Rahotanni daga Najeriya sun ce ana ci gaba da zaman zullumi a garin Wukari na jihar Taraba sakamakon wani harin 'yan bindiga a daren ranar Talata.

Bayanai na nuna cewa kimanin mutane takwas ne suka rasa rayukansu, a wani kauye da ake kira Nwunkyo-Kura, a cikin garin Wukari.

Mutane bakwai kuma sun rasa rayukansu a wani lamari mai kama da martani ga harin da aka kai tun farko a kauyen.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar ta Taraba, DSP Joseph Kwaji ya tabbatar da faruwar lamarin, amma ya ce tuni aka tura jami'an tsaro domin maido da doka da oda.