Chibok:Iyaye sun koka kan kokarin Sojoji

Wasu dalibai a Maiduguri Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Gwamnatin tarayya da ta jihar Borno sun rufe makarantu saboda hare-haren boko haram

Alummar garin Chibok a jihar Borno dake Nigeria, musamman iyayen 'yan matan da aka sace na cigaba da zaman zullumi saboda bacewar 'ya'yansu.

Lamarin da ya sa wasu iyaye suka taru a bakin kasuwar garin, domin nuna fushinsu a kan irin matakin da gwamnati ta ce tana dauka wajen kokarin gano inda daliban suke.

Wata uwa ta shaida wa BBC cewa "Fata na kawai Allah ya mayar mini da yarinyata ko a gawarta ko a menene"

Jami'an tsaro sun ce sun kara kaimi a kokarin da suke yi, na lalubo inda aka kai 'yan matan 100 da aka sace a daren ranar Litinin.

Ana dai zargin 'yan kungiyar Boko Haram da sace daliban, a lokacin da suke zana jarrabawa kamalla karantun sakandare.