Chibok: Iyaye za su shiga daji neman dalibai

Hakkin mallakar hoto AFP Getty
Image caption Wasu iyayen sun hada kudi domin neman taimakon 'yan banga, su nemo musu 'ya'yansu

Iyayen 'yan matan nan da aka sace a garin Chibok na jihar Borno sun ce, a shirye suke su shiga daji, domin nemo 'ya'yansu.

Iyayen sun shaida wa BBC cewa har yanzu fiye da 'yan mata 100 ba a san inda suke ba, baya ga dalibai goma da suka tsere suka je wani kauye kuma aka dawo da su gida.

Sabanin ikirarin da Kakakin rundunar sojin Nigeria Manjo janar Chris Olukolade ya yi a ranar Laraba, inda yace saura dalibai takwas ne kadai suka rage ba a kubutar da su ba.

Gwamnatin jihar Borno ta yi shelar dalan naira miliyan 50, ga duk wanda ya gano inda yaran suke, wanda 'yan Boko Haram suka sace a daren ranar Litinin.