Sabon nau'in kwayar cutar Ebola a Guinea

Hakkin mallakar hoto
Image caption Cutar ta bulla a wasu kasashen yammacin Afrika

Masana kimiya sun ce kwayar cutar Ebola da ta kashe mutane fiye da 100 a yammacin Afrika, sabuwar nau'i ce.

Wani bincike da wasu kwararrun masana na kasa da kasa suka gudanar da aka wallafa a Mujallar Lafiya ta Ingila, ya nuna cewar ba a san ainihin asalin kwayar cutar ba.

Sai dai a cewarsu ba daga wata kasa aka shigo da cutar ba, kamar yadda aka yi hasashe tun farko.

A watan daya gabata ne cutar ta barke inda ta kashe mutane da dama.

Galibin wadanda suka mutu a kasar Guinea da kuma Liberia ne.

Karin bayani