'Sabon hari da sinadarin Chlorine a Syria'

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Dubban mutane sun rasu a Syria

Masu fafutika a Syria sun wallafa abun da suka kira hujjojin da ke nuna cewa sojojin gwamnati sun kai wani sabon hari da sinadarin chlorine.

Wani hoton bidiyo da aka nuna ta Intanat sun nuna jami'an asibiti suna kokarin farfado da wasu matasa hudu, wadanda ga alama suka shaki sinadarin na chlorine.

Wakilin BBC ya ce masu fafitukar da suka wallafa bidiyon, wanda babu wata kafa mai zamnan kanta da ta tabbatar da shi, sun ce dukan matasan 4 sun shaki gubar ta chlorine ne a harin da sojojin gwamnati suka kai a unguwar Harasta dake arewa maso gabashin Damascus.

Wannan zargi dai ya zo ne kwanaki hudu, bayan harin da aka kai da sinadarin na Chlorine a Arewacin birnin Hama.

Gwamnati da 'yan adawa dai sun dora alhakin harin a kan junansu.

Karin bayani