Rabin al'umma ne suka yi zabe a Algeria

Hakkin mallakar hoto a
Image caption 'Yan adawa sun nemi a kauracewa zaben

Jami'an zabe a Algeria sun ce yawan mutanen da suka fito a zaben da aka gudanar ya haura kashi hamsin cikin dari da 'yar doriya.

Wannan adadin ya gaza da kashi ashirin cikin dari, in aka kwatanta da wadanda suka yi zaben 2000 da aka yi takaddama kansa.

Sai dai masu aiko da rahotanni sun ce akwai yuwuwar an zuzuta yawan fitowar jama'ar.

Shugaba mai ci, Abdul Aziz Bouteflika ne ake kyautata zaton zai lashe zaben, duk kuwa da cewa ba shi da koshin lafiya, kuma ma ya kada kuri'arsa ne daga kan keken guragu a ranar Alhamis.

Tuni dai wani jagoran 'yan adawa ya yi watsi da zaben, da ya ce an tafka magudi.

Karin bayani