Chibok: Sojojin Nigeria sun yi magana biyu

Hakkin mallakar hoto Nigeria Army
Image caption Babban Hafsan Tsaron Nigeria, Air Marshal Alex Badeh

Rundunar tsaron Nigeria ta amince a kan cewar ta yi kuskure a ikirarinta cewar an gano galibin 'yan matan da aka sace a Chibok.

Kakakin rundunar, Chris Olukolade da farko ya ce an ceto matan da aka sace su 129, sauran takwas ne kawai ke hannun 'yan Boko Haram, amma daga bisani sai ya janye maganar bayan da gwamnatin jihar Borno ta ce ikirarin sojoji babu gaskiya a ciki.

Kwamishin ilimi a Jihar ta Borno, Alhaji Musa Inuwa Kubo a hirarsa da BBC jim kadan bayan da ya ziyarci makarantar 'yan matan da ke garin na Chibok ya bayyana cewar dalibai 30 ne kawo yanzu aka gano daga cikin dalibai 129.

A cewar Kwamishinan, suna fatan za a ceto 'yan matan ba tare da wani abu ya same su ba.

Itama Shugabar makarantar 'yan matan, Asabe Kwambura ta ce an bude rajista a makarantar inda aka bukaci iyayen yara su je su rubuta sunayen 'ya'yansu da har yanzu ba a gani ba.

A jumlace dai a yanzu sauran dalibai 'yan mata 99 ake nema wadanda bisa dukkan alamu 'yan Boko Haram sun kaisu dajin Sambisa da ke kan iyakar kasar da Kamaru.

Masu sharhi dai na zargin gwamnatin Shugaba Goodluck Jonathan da gazawa wajen kare lafiya da dukiyar al'umma wanda a zahiri a yanzu kasar na kan hanyar da bata dace ba.

Sai dai gwamnatin Jonathan na cewar tana iyaka kokarinta.

Karin bayani