Sammacin kama matukin jirgin ruwa

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ana kokarin ceto wadanda ke cikin jirgin da ya nutse

Masu shigar da kara a Koriya ta Kudu sun nemi wata kotu ta bada sammacin kama matukin jirgin ruwan fasinjan nan da ya nutse ranar Laraba, wanda a sanadiyar haka ba a ji duriyar mutane 270 ba.

Haka nan kuma an nemi a bada sammacin kama wasu ma'aikatan jirgin ruwan su biyu.

Ana dai ci gaba da fuskantar matsaloli a aikin neman wadanda suka bacen.

Wasu gwanayen nutso da suka samu shiga cikin jirgin ruwan da ya nutse sun samu kaiwa ga dakin ajiye kaya ne, amma sun kasa matsawa gaba saboda rashin haske.

An dai tabbatar da mutuwar mutane ashirin da takwas.

An ga gawar mukaddashin shugaban makarantar da galibin daliban da suka bace suka fito, tana raito a kusa da inda iyalansu suke zaune.

Karin bayani